Labarai

Hisba ta kama matashin da zai sayar da kansa a Kano

Hisba ta kama matashin da zai sayar da kansa a Kano saboda rashin ganin sarkin waka Nazir M Ahmad

Advertisment

Hisba ta kama matashin da zai sayar da kansa a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama matashi nan mai shekara 26 wanda ya ce zai sayar da kan sa saboda talauci ya dame shi.

A ƙarshen makon jiya ne hoton Aliyu Na Idris ya karaɗe shafukan sada zumunta ɗauke da kwali yana neman mai sayensa kan kuɗi naira miliyan 20.

Kwamandan Hisba Haruna Ibn Sina ya tabbatar wa da BBC kama matashin, yana mai cewa abin da Aliyu ya aikata haramun ne.

”E mun kama shi ranar Talata kuma ya kwana a hannunmu saboda abin da ya akaita haramun ne a addinin Musulinci, ba ka da damar sayar da kanka a kowanne hali ka tsinci kanka” in ji kwamandan.

Aliyu Idris wanda tela ne, ya ce yana cikin matsalar kuɗi, don haka ne ya yanke shawarar sanya farashin naira miliyan 20 (dala 49,000 ko kuma fan 35,000) sannan ya yi wa mutumin da ya yi alkawarin sayensa hidima da zuciya ɗaya.

Kafin kama shi, Aliyu ya faɗa wa ‘yan jarida a Kano cewa: ”Na yanke shawarar sayar da kaina ne saboda talauci, idan na samu mai saye na shirya bai wa iyayena naira miliyan 10, na biya naira miliyan biyar a matsayin haraji ga gwamnati, naira miliyan biyu ga duk wanda ya taimake ni na samu mai saye na, sai na ajiye sauran don amfanin yau da kullum.”

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button