Soyayya Ruwan Zuwa! Idan So Hauka Ne Kada Allah Yasa Na Warkewa ~ Inji Ahmad mijin Zarah Buhari
Surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi, ya birge mabiya a kafofin sada zumunta da irin rayuwar soyayyarsa bayan ya rubuta wa matarsa Zahra Buhari kalmomi masu dadi kama yadda legithausa na ruwaito.
Da ya je shafinsa na Instagram, dan hamshakin dan kasuwa ya bayyana yadda yake haukan son matarsa.
Matashin ya wallafa hotonsa tare da Zahra inda ya raka shi da rubutu mai ratsa zuciya wanda ya kayatar da mabiya kafofin sada zumunta.
Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra
A cewar Ahmed, idan kasancewa cikin soyayya wani nau’in hauka ne, baya fatan ya sake samun hankali.
Ya rubuta:
”
“Kuma idan so hauka ne, kada Allah ya sa na sake samun natsuwa.”
Kalli wallafarsa a kasa:
View this post on Instagram
Ma’auratan sun birge ‘yan Najeriya matuka
Yawancin masu amfani da intanet suna mamakin yadda Ahmed ke nuna soyayya don haka suke nuna sha’awarsu ga dangantakarsa da Zahra Buhari.
Ga martanin wasu daga cikinsu a kasa:
Bighstudios:
“Ikon Allah. Wanene zai yi amfani da irin wannan kalaman a kaida .. Allah sai yaushe.”
Soulunraveled:
“Awwwww. Allah ya kiyaye soyayyar ku kuma ya daidaita muku shi❤️. ”
Ochuatom:
“Ina kaunar yadda yake son ta, son matar ka karfi ne ba rauni ba.”