Kuna Wahalar Kanku Ne Ina Gwamnati Zata Gane Ana kashe kashe Tunda Talakawa Ake Kashewa Basu Ba ~ Falalu Dorayi
T A ’A D D A N C I A
A R E W A
Idan kayi tallarsu lokacin da kake so a zabe su, Sai kuma kayi magana, lokacin da da suke kallo Jahohin mu na zubar da JINI.
#NorthernLivesMatter
Ya Ishi mutum takaici ganin yadda aka maida rayukan Al’umma kamar na kiyashi, kuma gwamnatocin mu na kallo. Sun gaza wajan kare Amanar da suka dauka.
Bawai baza su iya bane fah, ni nafi ganin ‘Akwai LAUJE cikin nadi’ domin cutar corona #Covid19 na zuwa, dukkan Shugabanin Kasa dana Jahohi suka dauki mataki akanta, wanda tasirin KISANTA bai quarter na kisan kiyashin da YAN TA’ADDANNAN suke ba.
In dai da gaske domin talakawanku kukai wancan aikin na CORONA, mai zai hana kuyi irinsa a bangaren TA’ADDANCI.
Babu wata Al’umma da zata tafi akan wannan dabi’ar ta halin ko In kula daga shugabanninta, ace akwai ADALCI. Nafi ganin Anfi bawa Maganar baki muhimmanci akan AIKI. Domin aiki na gaske bazai bawa BOKO HARAM damar cigaba da kai hare-hare ba, MASU GARKUWA su dinga abin da suke so a hanya, BARAYIN SHANU su afkawa garin mutane su debi awowi suna barna da cin rafin ‘Yan mata da matan aure a gaban mazajensu da iyayensu, babu keyar jami’anmu.
Wasu mabiya Jagororinmu suna cewa ana ta kokari fah, Eh, tunda gidanka ba YINWA, Yin FYADE ga matar aure, bai biyo ta gidanka ba, kuma baku taba biyan kudin FANSA ba. Ku fadi gazawar Jagoran ku ta inda ya gaza, ku nuna masa inda zai gyara shine so na GASKIYA.
Idan ba zai yiwu ba, su rubuta sunayen su a gidan tarihi. Suna cikin Yan Siyasar da suka sami dama, da kudi da komai, amma sun kasa tsare rayukan al’ummar ku. Wannan kuwa tuhuma ce mai girma a ranar KIYAMA.
Wani Masani yace “kuna wahalar da kanku ne, ta ina gwamnati zata gane ciwon da kuke ji bayan akan talaka kawai abin yake karewa,” Yace “Da ace KISA da FYADE da KWASHE DUKIYA da ake ya shafe su, Da wani zancen ake ba wannan ba, To koma menene ai Qur’ani mutum ya saba Yai rantsuwa.
Bamu da bakin magana Idan mulkin nan ya kare. Idan ka dauke @muhammadubuhari , duk fannin tsoro hannun Mutanen arewa yake. kusan duk Yan arewa ya nada domin su dubi matsalarmu. kuma idonsu biyu ba bacci suke ba.
Ranar Nadama ba dadi.
Ya Allah ka shiryemu
Juma@tMbrk #sisters & #brothers
#falaludorayi





