Kannywood
Ganduje Ya Nada Jarumi Ishaq Sidi Ishaq Muƙamin A Gwamantinsa


Advertisment
A yau din nan ne Majiyarmu ta samu labarin babban mai bada umurni a masana’antar Kannywood ya samu mukami daga gwamnatin kano karkakshin Dr Abdallahi Umar Ganduje mukamin mai baiwa gwamna shawara kamar yadda falalu dorayi yayi posting wanda shima ya nuna cewa umar gombe ne ya fara wallafa wannan labari kamar yadda zaku gani tare da shi.
“Muna taya director Ishaq Sidi Ishaq
@sidishaqq murnar samun matsayin Senior Special Assistant ga Gwamnan Kano. Dr. Abdullahi Umar Ganduje a bangaren Kano State Creative Industries.
Akwai Kalubale, sai kayi da gaske.
Domin tukunyar sama ce ragamarta ta dawo hannuka.
Allah ya baka ikon aiki da adalci.”

