Labarai

HOME OF SOLACE: Bazamu bari wasu suzo Kano suyi taron baɗala ba – Hisbah

Advertisment

Jaridar Amintacciya: Hukumar Hizba ta jihar Kano tasha alwashin hana Group ɗin HOME OF SOLACE taro a Kano da sunan taron Sada zumunci.
Shugaban hukumar Hizba na Kano Sheikh Muhammad Harun Ibn Sina, ne ya bayyana haka yayin tattaunawar sa da manema labarai.
AMINTACCIYA: Ta rawaito cewa, Ibn Sina yace, Hukumar Hizba hukuma ce dake umarni da kyakkyawa da kuma hani da mummuna, sulhu tsakanin al’umma, ko kaɗan Bazamu amince ba bazamu lamunta ba wasu su shigo su gurɓata mana tarbiyyar yaranmu ba.
Yaci gaba da cewa, mun sami labarin wasu gungun mutane, sunyo shiri wai zasu zo Kano suyi taro da sunan taron Sallah to babu shakka bazamu bari ai taron baɗala da sunan taron Sallah ba – inji shi.
Wani mai suna Hasnul Basari ne dai ya shigar da Group ɗin ƙara kan wani taro da sukace zasu yi, kuma za’a tara mata da maza guri ɗaya wanda a cewar sa taron baya kan tsari.
Jama’a da dama ne dai sukai ta kiraye kirayen a hana taron, sai dai masu Group ɗin sun cigaba da shirye shiryen su, saboda a cewar su zasu yi taro ne na sada zumunci.
Ga bidiyo nan domin saurare daga bakinsa.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button