Labarai

Yanzu-yanzu: Buhari ya bada umurnin a bindige duk wanda aka gani da AK-47

Advertisment

– Mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ne ya bayyana hakan a cikin wata hira da aka yi da shi
– Shehu ya ce Shugaba Buhari ya bada umurnin ne domin kawar da yan bindiga, masu garkuwa da sauran bata gari da suka ki mika wuya
Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin tsaro da su harbi duk wani da suka gani dauke da bindigar AK-47.
Kamar yadda legit na ruwaito.Shehu ya bayyana hakan ne cikin wata hira da BBC ta yi da shi, ya ce shugaban kasar ya bada umurnin a kawar da yan bindigan da suka ki mika wuya su ajiye makamai.
A watan Nuwamba, Alhaji Sa’ad Abubakar, Sarkin Musulmi ya ce yan bindga suna yawo dauke da AK47 a sassa daban-daban na arewacin kasar.

A kokarin samar da zaman lafiya da tsaro a Zamfara da wasu jihohin arewa, Shehu ya ce gwamnati za ta yi amfani da karfin bindiga kan wadanda suka ki su mika wuya.
“Shugaban kasar ya umurci jami’an tsaro su shiga dazuka su bindige wanda suka gani dauke da muggan makamai kamar AK-47,” ya ce a hirar da aka yi da shi.
 
Ya bada umurnin a harbe duk wani da aka gani da muggan makamai nan take.”
Har wa yau, kakakin shugaban kasar ya kuma ce gwamnatin tarayya ta kafa dokar hanawa jirage keta sararin samaniyar jihar Zamfara ne bayan ya samu bayanin sirri da ke nuna cewa ana kai wa yan bindiga makamai ta hanyar amfani da jirage na masu zaman kansu.

Ya kuma ce ana amfani da jiragen ana tafiya da gwala-gwalai zuwa Dubai, hakan yasa shugaban kasar ya bada umurnin a dakatar da hakkar gwala-gwalan.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button