Labarai

Sarkin Musulmi ya yi watsi da shirin muƙabala da Malam Abduljabbar


Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi watsi da shirin Gwamnatin Kano na shirya muƙabalar malamai.
Kamar yadda Freedomradio na ruwaito.Sarkin ya bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ƙungiyar Jama’atu Nasril Islam da ya ke shugabanta ta fitar ta hannun babban sakataren ta Dr. Khalid Abubakar Aliyu.
Sanarwar ta ce, a baya ta yaba wa Gwamnatin Kano dangane da matakin da ta ɗauka na dakatar da Malam Abduljabbar Kabara daga karatu tare da rufe masallacinsa.


A cewar ƙungiyar, la’akari da kalaman malamin to babu buƙatar shirya wani zaman muƙabala tare da shi.
A ƙarshe JNI ta ce, ita da mambobinta sun cimma matsaya kan cewa, ba za su shiga duk wani taro da aka shirya domin tattauna wa da malamin ba.

Nasril Islam ta ce, tana fata Gwamnatin Kano za ta yi la’akari da wannan matsaya da ta ɗauka domin sauya matsaya.

A ranar Lahadi ne Gwamnatin Kano ta shirya gabatar da wannan muƙabala da ta ce, Mai Alfarma Sarkin Musulmi zai zamo babban baƙo.

Ci gaban wannan labari zai zo nan gaba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button