Labarai
Da Dumi Dumi : An kama wani dan majalisa da hannu a Boko Haram
Advertisment
An kama wani dan majalisar kasar Kamaru da ake zargi da hannu a Kungiyar Boko Haram.
Tsohon dan majalisar kasar daga jam’iyyar CPDM ya shiga hannu ne bayan da aka kama wani dan uwansa, Talba a Kolofata da shanu 10.
Da aka bincikeshi yace Najeriya zai kaisu, da bincike yayi tsanani shine ya bayyana cewa, dan majalisa, Blama Malla ne ya aikeshi ya kaiwa Boko Haram sun shanun
An dai kamasu duk ana kuma kan bincikensu kamar yanda HumAngle ta ruwaito. A baya dai wani dan majalisar, Yegue Djibril yayi zargin cewa akwai ‘yan Boko Haram a majalisar ta Kamaru amma bai iya fadar sunayensu ba.




Masha Allah