Shirin Horas da Matasan Najeriya a Sana’o’in Hannu: Gwamnatin Tarayya da ITF Sun Kaddamar da “Skill-Up Artisans (SUPA)”


Gwamnatin Tarayya, tare da haɗin gwiwar Hukumar Industrial Training Fund (ITF), ta kaddamar da shirin horar da matasan Najeriya a fannoni daban-daban na sana’o’in hannu domin ƙarfafa dogaro da kai. Shirin ya kasu gida uku:
Ƙwararrun Masana (Skilled Artisan) – Wadanda ke da ƙwarewa a wata sana’a kuma suke son shiga shirin.
Masu Sha’awar Koyo (Intending Artisan) – Wadanda ke son koyon sabuwar sana’a.
Cibiyoyin Horaswa (Training Center) – Masu bada horo a fannin sana’o’in hannu.
Bayan kammala shirin, mahalarta za su sami takardar shaidar kammalawa tare da tallafin fara kasuwanci domin su ci gaba da aikin da suka koya.
Sana’o’in da za a koyar sun haɗa da:
– Gina da Gine-gine (Building and Construction)
– Gudanar da Masauki da Otal (Hospitality Management)
– Harkar Wutar Lantarki (Power)
– Fata da Kayan Fata (Leather Works)
– Noma da Harkokin Noma (Agric/Agro Allied)
– Zanen Kaya da Dinki (Fashion Design)
– Fannin Kwamfuta da Sadarwa (ICT)
– Sana’o’in Hannu da Fasaha (Arts and Crafts)
– Gyaran Kayan Amfani (Appliance Service Technician)
– Kawata Ciki da Tsara Gida (Interior Design)
– Gyaran Motoci (Vehicle Auto Services)
– Kula da Fata da Kyau (Cosmetology)
– Gudanar da Muhalli da Tsare-tsare (Facility Management and Planning).
Yadda za’a cika (How To Apply)
Ga masu sha’awa da ya cika ka’idoji sai su latsa maɓali (link) da ke kasa domin cikawa