KannywoodUncategorized

Gwamnatin Kano ta maka mawaƙi Rarara a gaban kotu

Advertisment

Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta kai mawakin siyasa Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara ƙara a kotu bisa sakin wata waka da hukumar ta de bai kawo ta tantance ta ba.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya aikawa da manema labarai, hukumar ta ce tun tuni ta aikawa da mawakin sakon korafi dangane da sabuwar wakar daya saki batare da ya kawo an tace ba, amma ya ƙi bata amsa.

A cewar sanarwar, hakan ne ya sa hukumar ta garzaya gaban kotun.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa tuni kotun ta aikawa da mawakin takardar sammaci sai dai ba’a ga fuskarsa ba ayau 13 ga watan nuwamba a yayin zaman kotun.

Tun kafin wannan lokacin bayan sakin sabuwar wakar Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jihar Kano ta turawa mawakin sakon neman ba’asi ta hanyar sakon karta kwana, saide har kawo ya wannan lokaci mawakin bai maidowa da jukumar amsar sakon ba.

– Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button