Bidiyon yadda yan bindiga su ka ciyar da karnukan su da gawar ɗan uwa na a Sakkwato – Malamin addini
Fitaccen Malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Bashar Danfili, ya roki jama’a su taimaka musu da tallafin kudi bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan uwansa.
Daily Trust ta rawaito cewa a wani gajeren faifen bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, Malamin ya ce mutanen da aka sace sun hada da wani mutum da mahaifiyarsa da kishiyarta da matasansa biyu da kuma ƙanwar sa.
Ya ce, ƴan bindigar sun nemi kudade masu yawa, wanda a yanzu sun kasa hadawa, inda ya kara da cewa, wa’adin da ƴan bindigar suka basu na kara kusanto wa.
Malamin ya ce: “Yan bindiga sun sace makusanta na. Ba sai na fadi sunansu ba.
“Suna kan hanyar su ta zuwa wani kauye a yayin da aka kwashe su.
“Sun kashe direban motar kuma suka baiwa karnunaka naman sa suka cinye.
Domin kallon bidiyon shiga nan
” Sai dai ragowar mutanen har yanzu suna hannunsu, ciki har da miji da matan nasa da mahaifiyarsa.
“Yan bindigar sun bukaci miliyoyin kudade, wanda mun kasa hadawa.
” Ni Malami ne, bani da komai. Aiki na shi ne koyar da al’umma da littafan da kuke gani a baya na.
“Kuma sun bamu wa’adin lokacin da za a kai kudin, idan ba a kai ba zasu kashe su gabadaya.
” Nasan zasu iya yin hakan, duba da abinda ya faru da Sarki a kwanan nan.
“A don haka nake neman taimako daga al’umma domin biyan kudin fansa don sako su”.
Daily Nigerian Hausa