Labarai

Ana kukan yunwa: Harajin da ƴan Nijeriya ke biya ya yi kadan – Bill Gates

Fitaccen Attajirin nan na duniya, Bill Gates wanda shi ne shugaban gidauniyar Bill da Melinda, ya ce harajin da ake karba a Nijeriya ya yi kadan.

Bill Gates ya yi bayanin hakan ne a taron tattaunawa na matasa kan samar da abinci mai gina jiki a Abuja a jiya Talata.

Daily Trust ta rawaito cewa, Attajirin dan kasar Amurka yazo Nijeriya ne domin halartar taruka.

Da yake jawabi a taron, Bill Gates, ya ce karancin haraji da ake karba yana haifar da kalubalen kudi a fannin lafiya da ilimi.

Ya ce domin yan kasa su samu karfin gwiwa kan kokarin gwamnati na kula da lafiya dole ne a tabbata ana tafiyar da kudaden da ake warewa fannin lafiya a yadda ya dace.

Bill Gates ya ce, ” Tsawon lokaci akwai shirye shirye ga Nijeriya wajen samar da kudade ga gwamnati fiye da yadda ake a yanzu. Abinda Nijeriya ke karba na haraji ya matukar kadan”, inji shi

Daily Nigerian Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button