Hukumar kwallon kafar Turai UEFA na Shirin karrama Cristiano Ronaldo, a matsayin gwarzon kwallon kafa a nahiyar turai
Karramawar mai daraja ta ɗaya za ta tabbatar da matsayinsa na ɗan wasan da ya fi zura kwallaye a gasar zakarun Turai.
Shugaban UEFA Aleksander Čeferin ne zai ba da lambar yabon ta musamman yayin wani ƙatsaitaccen bikin fitar da jadawalin gasar zakarun Turai na wannan kaka ta 2024/25 ranar Alhamis, a dandalin Grimaldi da ke Monaco na ƙasar Faransa.
Cikin wata sanarwa da UEFA ta wallafa a shafinta na intanet a ranar Talata, ta bayyana nasarorin da Ronaldo ya samu a gasar zakarun Turai da suka haɗa da kwallaye 140 da ya ci a wasanni 183, sun sake fayyace tarihin gasar. RFIHausa na ruwaito.
A cewar Hukumar Kwallon Kafar Turan Ronaldo a matsayinsa na ɗan wasa daya tilo da ya zura kwallo a wasannin ƙarshe na gasar daban-daban har uku da kuma ɗage kofin biyar, wannan karramawa ta tabbatar da tarihin da ya bari a fage kwallon kafa, ga zuriyar ƴan wasan kwallon kafa na gaba.