Labarai
Tsada Rayuwa: Sheikh Guruntum ya gwangwaje dalibansa da kyautar abinci da kuɗi


Advertisment
Shahararren malamin Addinin Musuluncin nan dake Jihar Bauchi, Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum, ya gwangwaje dalibansa akalla 50 da kyautar kudi tare da katan din Taliya.
Kudin da malamin ya rabawa daliban nasa sun fara daga Naira dubu 10, 20, da kuma 30. Yayin da kowanne cikin dalibai 50 din ya rabauta da katan din taliya.
Wani daga cikin manyan daliban malamin ya shaida mana cewa, wannan rabon da Malamin ya yi, ya takaita ne kadai ga dalibansa, amma malamin yana daf da sake yin wani rabon wanda zai shafi al’umma gaba daya.
Ba wannan ne karon farko ba, ko a baya an saba ganin malamin yana shirya ciyrwa ta musamman ga al’umma, musamman a watan azumin Ramadan.