Labarai

Ƴan bindiga sun kai harin bazata a jihar Sakkwato, sun kashe sun dauki mutane sama da 30

A jiya litanin da misalin karfe 9:30pm na dare yan bindiga sun kai hari a kauyen garin gwaddodi da ke cikin ƙaramar hukumar mulkin Rabah da ke gabashin Sakkwato.

Harin na bazata ne wanda a lokacin kowa yana yawonsa gudanar da hada hada kwatsam sai sun kaji ƙarar halbin bindiga nan ne mutane sunka fara neman mafaka.

A cikin rahoton da majiyarmu ta samu ga mazauna garin sun ce yanzu haka sun tafi da mutum yakai 33 a bisa lissafin jama’a gari da sunka yi, ba tsohuwa ba yaro,  harda masu ciki da goyo, sunka kashe wani Dattijo da yace shi bazai ba.

Ga yadda sunkayi da barayin har sunka kashe shi nan take :

“Ni babu inda za ni domin ni talaka ne bani da komai, sunka ce kai dai mu tafi ,yace lallai bazai tafi ba sai da ku kashe ni, nan take sunka halbe shi sunka bar gawarsa a bayan gari.”

Mazauna garin suke gayamana cewa inda abin yazo da sauki zuwan jami’an tsaro na sojoji sun kawo dauki nan take sunka kore su sunka bar garin, abin ban takaici shine akwai yarinyar da ta haihu ko suna ba’a yi ba, sun yafi da uwar sun bar jinjirin.

Allah ya jiƙansa ya kuɓutar da wadanda sunka dauka, Allah ya zama lafiya kayi mana maganin wannan masifa Amin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button