Tabbas ya kamata a dawo da Sanusi lamido sarkin kano – Naziru sarkin waka


Fitaccen shahararren mawakin nan na sarakuna, siyasa da ma soyaya Naziru m Ahmad sarkin waka san kano ya bayyana cewa yakamata kwankwasiyya ta tsaya taganin shin miyasa anka sauke sarki sanusi daga kujerarsa.
Kawai saboda yace lallai a baiwa abba kujerarsa a wancan lokaci shine musabbabin abin da ya sanya anka sauke sa.
Wannan shine karo na farko da sarkin waka yazo yana kariyar wani a fadan bakinsa da yake fira da Dclhausa radio.
Shin kana ganin dawowar sarkin sanusi wanda yake bawa gwamnati shawara a cire tallafi yadda rayuwa zata musu tsada zasuyi marhaba da dawowarsa?
“Ae in ba’a maraba kai kasani duk wanda yake jihar kano ne a dawo da Sarkin kano inda talaka ne yasan amfaninsa, wanda kullum ba dare ba rana yana bayar da dukiyarsa a dafa abinci a chi ai ba abin da yakai wannan , amma wasu labarai da muke ji duk ba dadin ji ba dadin fada”- inji Sarkin waka.
Akwai maganganu da sarkin waka yayi da zaku saurare su a cikin wannan faifan bidiyo da yake kasa.