Kannywood

Nabar Kannywood daga yau – Malam Ali kwana casa’in

Fitaccen jarumi nan a masana’atar Kannywood abdul sahir wanda anka fi sani da Malam ali kwana casa’in ya bayyana cewa daga yau ya bar kannywood daga yau Alhamis.

Abdul sahir ya bayyana hakane bayan da ya saurari firar da akayi da shugaban tace fina finai Abba El-Mustapha wata fira da ankayi da shi a gidan rediyo freedom radio kano da ankayi masa tambaya cewa:

Minene matsayar kannywood da Abdul sahir?

“Abba El-Mustapha yaka amsa cewa abdul sahir bai fito ya bada hakuri ba tun daga lokacin da anka dakatar da shi”

Ta dalilin haka abdul sahir wanda anka fi sani malam ali kwana casa’in ya fadi irin alakar da ke tsakaninsa da abba El-Mustapha wanda ya sanya yayi maganganu da dama akan wannan maganar tashi ta cewa ya bar kannywood.

Ga bidyon nan domin sauraren abin da yasa ya fadi haka.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA