Labarai

Yanzu Yanzu : Majalisar Dokokin Kano Ta Rushe Masarautun Da Ganduje Ya Kirkiro

Advertisment

Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta amince gyaran dokar da ta samar da sabbin masarautu a jihar tare da rushe masarautun da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya kirkiro.

Wannan na zuwa ne bayan zama da majalisar ta yi a yau Alhamis tare da yin duba a kan dokar da ta kirkiro sabbin masarautun.

Zaman majalisar na yau, wanda shi ne zama na uku, majalisar ta amince da kundirin gyaran dokar ta kafa masarautun jihar guda biyar, wanda aka samar a karkashin gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.

Tun da fari gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da zai sanya hannu idan majalisar ta amince da gyaran dokar.

Shugaban masu rinjaye kuma wakilin mazabar Dala, Hussein Dala ne, ya gabatar da kudirin gyara dokar a yayin zaman majalisar na ranar Talata

Ganduje Ya Tsige Sanusi A 2020

A shekarar 2020, kafin a tsige Sanusi II, Ganduje ya rattaba hannu kan wata doka mai cike da cece-kuce, wadda ta raba masarautar Kano zuwa masarautu biyar.

Matakin dai ya haifar da cece-kuce da rarrabuwar kawuna a tsakanin masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar.

Magoya bayan Kwankwasiyya, sun yi ta kiranye-kiranye kan a mayar da Sanusi II kan karagar mulki tare da rushe masarautun Bichi, Gaya, Rano, da kuma Karaye.

A gefe guda kuma akwai wasu ƙungiyoyi da ke adawa da rushe sabbin masarautun, inda suke kallon yunkurin a matsayin wata gaba ta yin ramuwar gayya.

Leadership Hausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button