Sharhin Fina Finai : Sharhin Fim Din ‘Meera’
Suna: Meera
Tsara Labari: Abdullahi Amdaz
Kamfani: A Skuare Century Nigeria Limited
Shiryawa: Hamisu Muhammad
Bawasa Umarni: Abu Sarki
Sharhi: Hamza Gambo Umar
Jarumai: Adam A. Zango, Hauwa Waraka, Umma Shehu, Fati S.U, Aisha Muhammad, Ladidi Tubles, Amina Amal. Da sauransu. A farkon fim din an nuna Meera (Aisha Muhammad) tare da jami’an tsaro wadanda suka kamo ta daga gidan iyayen ta suka saka a motar su sannan suka kai ta ofishin su.
Bayan sun kulle ta a ofishin su ne suka gabatar da bincike sannan suka mika ta ga kotu aka soma shari’a gami da tuhumar ta da laifin kashe iyayen ta da kannen ta mata guda biyu tare da ‘yar kanin mahaifin ta gaba daya. Meera ta musanta zargin da ake mata na cewar itace ta kashe su, yayin da kanin mahaifin ta ya bayyana a gaban alkali gami da tabbatar wa da jama’a cewa Meera ce ta kashe su, anan fa ya bada dalilin sa na fadin hakan inda ya bayyana cewar Meera macece budurwa me son shagala wadda kuma ba ta bin umarnin iyayen ta, sau da yawa takan fita yawon shakatawa da samari har a club sannan kuma ta kan sha kayan maye masu gusar da hankalin mutum sannan ta ci zarafin wadanda taga dama a cikin jama’a. A wasu lokutan tana buge mutum da motar ta kuma tayi tafiyar ta ba tare da wata damuwa ba, sai dai jama’a su dauko wanda ta buge da mota su kawo shi wajen mahaifin ta yayin da shi kuma zai bada kudi a kula da lafiyar wanda ta buge din, halin Meera ne yasa mahaifin ta yayi yunkurin yi mata auren dole amma sam ta nuna bata amince ba, a wasu lokutan ma har makami mahaifin ta yake dauka da nufin halaka ta saboda bakin cikin da take cusa masa, mahaifiyar Meera tana yawon yi mata fada gami da nasiha akan ta gyara halayen ta sai dai hakan bai sa Meera ta saduda ta gyara halin nata ba. Sai dai kuma daga bisani sai Meera ta yi tunanin abubuwan da take aikatawa ba su dace ba, hakan ne yasa tazo gida ta roki gafarar mahaifin ta gami da yi masa alkawarin cewa za ta auri duk mijin da ya zaba mata. Kwatsam a wannan ranar ne kuma bayan faruwar haka sai aka wayi gari an kashe iyayen Meera gaba daya tare da sauran ‘yan uwan ta, dalilin hakan ne yasa aka kawo ta kotu saboda ana zargin cewa ita ce ta kashe iyayen nata.
Bayan an gama gabatar da shaidu da hujjoji masu karfi sai alkali ya tabbatar wa da jama’a cewar Meera ce ta kashe iyayen da ‘yan uwan ta, dalilin hakan ne yasa aka yanke mata hukuncin zama na har abada a gidan yari, wato (Daurin Rai Da Rai) haka aka tafi fa Meera gidan yari aka saka ta a cikin sauran mata masu manyan laifuka makamanta da nata. Meera ta soma fuskantar tsangwama da hantara daga wajen abokan zaman ta da ke dakin ta na bursun, suka soma dukan ta gami da sanya ta aikin kaskanci da wahala, kamar su wankin bandaki da debo musu ruwa, idan ta tsaya yin gardama su dake ta.
Hakan ne yawa ta soma tuna rayuwar ta ta bata da irin rashin biyayyar da ta yiwa iyayen ta. Wata rana Meera bata da lafiya sai daya daga cikin jami’an tsaron gidan yarin Nura (Adam A. Zango) yazo ya duba ta yasa aka bata magani, tana tsaka da larurar ne ‘yan dakin da take su Raskatu (Hauwa Waraka) da (Umma Shehu) da (Fati S.U) suka uzzura mata akan sai ta yi musu aiki, ganin taki yarda ne suka soma wulakantata wanda hakan ya sa Nura ya iso wajen yaci musu mutunci gami da fadawa Meera lallai sai ta tsaya da kafarta ta kwaci ‘yancin kan ta.
Jin hakan ne ya sa Meera ta daina ragawa su Raskatu har wata rana ta dauki dutse ta bugawa Raskatu aka gami da yi mata gargadin ta daina raga musu gaba daya, faruwar hakan ne yasa Raskatu ta tanadi reza ta ajiye a dakin ta da nufin daukar mataki akan Meera, amma da Nura ya fahimci hakan sai yasa aka kama Raskatu aka kai ta dakin horo. Nura da Meera suka soma soyayya wadda har suka shaku suka soma tunanin auren juna, dalilin hakan ne yasa Nura ya samarwa da Meera aiki a dakin ajiye gawa da nufin idan an saka gawa a cikin akwati to tayi dabarar shiga ciki a hada da ita a fitar gaba daya, sannan yayi mata alkawarin zuwa kabarin da aka binneta cikin sauri don fitar da ita, da farko Meera bata amince ba sai daga baya ta yarda da shawarar shi, sai dai kuma batayi nasarar aikata hakan a karon farko ba sai a karo na biyu sanda babu idon jama’a, hakan yasa tayi amfani da wannan damar ta shige cikin akwatin gawa ta rufe.
Abubuwan Birgewa:
1- Labarin ya nishadantar kuma ya fadakar, sannan ya tafi kai tsaye zuwa ga sakon da ake son isarwa.
2- Camera ta fita radau, haka ma sauti ba laifi. Kurakurai: 1- Ya kamata a rubuta sunan fim din a Hausance wato “Mira” ko “Amira” ba “Meera” ba, domin an nuna cewar fim ne wanda ke wakiltar Hausawa, kuma bahaushen labari wanda aka yi sa da yaren Hausa.
2- A farko an nuna lauya (Abbas Sadik) yana tuhumar Meera dalilin da yasa ta kashe iyaye da ‘yan uwan ta, amma daga baya sai me kallo yaji lauyan ya sake tambayar ta da cewar ko shaye-shaye tayi ne da har aka shiga gidan su aka kashe iyayen ta bata sani ba? Shin dama lauyan bai tabbatar da cewar Meera ce tayi kisan ba da har a farko ya tuhume ta akan hakan? Idan kuma salon tambayar ne yazo masa a haka, to ya dace ya nuna cewar ana zargin ta da kashe iyayen ta amma ba kai tsaye ya lika mata alhakin kisan ba.
3- Lokacin da alkali ya bukaci ganin inspector abbas wato jami’in tsaron da suka gudanar da bin
cike bayan an kashe iyayen Meera, Camera tayi rawa a lokacin da inspector abbas ya fito zuwa gaban kotu don fadin abinda ya sani.
4- Har fim din ya kare ko sau daya ba’a nuna kannen Meera guda biyu da ‘yar kanin mahaifin ta da aka ce ta kashe su ba, ya dace ko sau daya ne a nuna su cikin labarin ta da aka bayar kafin faruwar kisan da aka yi, ko kuma a nuna su lokacin da aka kashe su din, hakan sai yafi gamsar da mai kallo fiye da ambaton sunayen su a baki. Domin kuwa gani ya kori ji.
5- An nuna Raskatu (Hauwa Waraka) da sauran abokan zaman ta a dakin su na gidan yari wato (Fati S.U) da (Umma Shehu) cikin dare suna kwance da kayan gida, wato atamfa ba uniform din su na ‘yan bursun ba, shin dama sun shigo gidan yarin ne da wasu kayan sawar na marasa laifi? 6- Dajin da aka nuna su Meera a gidan yari suna daukar duwatsu da ciyayi bai yi kama da bangaren gidan yari ba, yafi kama da gefen hanya, domin me kallo yaga tsirarun ababen hawa da sauran jama’a akan mashina su na kai kawo tamkar hanyar wucewar kowa da kowa.
7- Lokacin da Meera ta bude akwatin dake dauke da gawa ta shiga ta kwanta, yanayin yadda ta shiga cikin akwatin bai yi kama da akwatin da ke dauke da wata gawar mutum din a ciki ba, hakan ya fi kama da akwatin da babu kowa a cikinta.
Karkarewa:
Fim din ya nishadantar, kuma ya fadakar, domin an nuna illar sabawa iyaye wanda hakan yakan iya jefa mutum cikin wata musiba, sai dai kuma labarin bai dire har karshen sa, akwai abubuwan da ba’a karkare su ba, idan kuma za’a yi cigaban fim din ne to ya dace a karshen fim din a bayyana hakan ko da a rubuce ne don a fitar da me kallo daga cikin.