AddiniLabarai

Ladabin Rubutun Hausa akan Manzon Allah, Tsira da Aminci Allah su Tabbata a Gare Shi

Ko wani yare akwai yadda ake amfani da shi da yadda ake kira ko rubuta abubuwa masu girma da daraja bisa tsarin girmamawa ta addini da al’adar
mutanen da ke amfani da wannan yaren.

Ba zan tsaya in kawo misalai ba, zan tafi gadan-gadan bisa fayyace wasu rubutu da ake yi akan rubutu akan Manzon Allah Tsira da Aminci Allah su tabbata a gare Shi, wanda sam ba dai-dai ba ne, misali;Ladabin Rubutun Hausa akan Manzon Allah, Tsira da Aminci Allah su Tabbata a Gare Shi.

Ba a cewa “Ko” Manzon Allah! Amfani da kalmar “Ko” a wajen rubutu ko magana akan Manzon Allah kuskure ne ƙwarai!
Duk wani masanin harshen Hausa ya san ita kalmar “Ko” kalma ce ta inkari ta nuna gazawa da raini ga wanda ake magana akai a yawancin lokaci.
Misali a ce “Ko”waye shi bai isa ba”
“Ko ub*nsa ne ya zo, sai mun faɗa masa gaskiya”

Ba a cewa “Shi ɗin” Ba a amfani da kalmar Shi ɗin akan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi su tabbata. Don a tsarin kalmar sam ba girmamawa. “Shi ɗin” ana afani da ita ne a gama garin mutane. Misali: “Shi ɗin” ne ya faɗa” “Ko “shi ɗin” bai ce ka tafi ba” Don haka a tsarin girmamawa ta rubutu da furuci a Hausa ko Sarki ba a cewa “Shi ɗin” sai da a ce “Sarki ne ya faɗa” bare kuma ai jingina wannan kalmar ga Manzon Tsira da Aminci Allah su tabbata a gare Shi.

Ba a lissafo jerin sunaye kawai a haɗo da sunan Manzon Allah (S.A.W) a jera su. Misali: Da Usman da Umar da Abubakar da Manzo Allah (S.A.W) da …. yin hakan kuskure ne. Sai dai ka ce Manzon Allah (S.A.W) sannan ka lissafo sauran wanda za ka lissafo.

Ba a rubuta ko cewa Manzon Allah(S.W.A) na Aliyu ko na Aishatu, sai dai a ce Aliyu na Manzon Allah (S.A.W) ko Aisha ta Manzon Allah (S.A.W).

Akwai kurakurai da yawa da ake yi akan rubutun Hausa wanda sam ba su da tsari da girmamawa ga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare Shi. Ameen.

Mukhtar Sipikin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button