Labarai

ASUU ta kara tsawaita yajin aikinta da makonni 8

Advertisment

ASUU ta kara tsawaita yajin aikinta da makonni 8Kungiyar malaman jami’o’in ta Najeriya, ASUU, ta sanar da tsawaita wa’adin yajin aikin da suka tafi zuwa makonni 8 sakamakon rashin cimma matsaya da gwamnati kan bukatunsu kamar yadda jaridar Bbchausa na ruwaito.
ASUU ta shiga yajin aikin ne sakamakon abin da ta bayyana a matsayin gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen aiwatar da jarjejeniyar da suka kulla a baya game da yadda za a inganta harkokin karatun jami’a na kasar.
Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau jami’i ne a kungiyar ta ASUU, ya ce sun dauki matakin kara wa’adin ne domin bai wa gwamnati damar cimma sahihiyar matsaya, ta yadda ba sai sun kara tafiya wani yajin aikin nan gaba ba.
Ya ce makonni 8 sun wadatar matukar gwamnatin da gake ta ke kan daukar matakin da ya dace.
ASUU dai na ganin yajin aikin ne hanyar karshe da take bi domin tilasta wa gwamnatin Najeriya biya mata bukatunta.
Tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamanatin Najeriya na tsawon wata guda.
Yajin aikin malamai a Najeriya ya fi yin tasiri a kan dalibai wadanda ke tsintar kansu cikin damuwa, dalilin da ya sa wasu ke ganin ya kamata kungiyar ta sauya salon tunkarar rikicinta da gwamnatin kasar ba sai lallai ta hanyar yajin aiki ba.
Wasu bayanai sun nuna cewa kungiyar ta ASUU ta daka yajin aiki sau 15 tun bayan komawar Najeriya mulkin dimokuradiyya a 1999, lamarin da kan jefa harkokin karatu cikin mawuyacin hali.
Ga hirar jaridar Bbchausa da tayi da Farfesa Abdulkadir Muhammad Danbazau

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button