Mutanen Gombe Sun Kai Karar Ministan Sadarwa Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami Kotu Akan Lallai Sai Ya Fito Takarar Neman Gwamnan Gombe A Zaben 2023
Wasu mazaunan jihar Gombe masu kishi sun shigar da ƙara gaban babbar Kotu kan Minista harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Pantami, domin tilasta masa ya tsaya takarar gwamna a 2023.
Mutanen daga gundumomi 114 dake faɗin jihar Gombe sun shigar ƙarar ne ranar 21 ga watan Maris, 2022, kamar yadda shafin daily news hausa sunka ruwaito cewa Jaridar Punch ta rahoto.
Shari’ar wacce aka shigar da Pantami da kuma jam’iyyar APC mai mulki zata gudana ne ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a A.Y Abubakar na babbar Kotun jihar Gombe.
Da yake jawabi a wurin taron manema labarai, shugaban tawagar mutanen da suka shigar da ƙarar, Muhammad Abdullahi, ya ce tsohon shugaban NITDA ya nuna kyakkyawan jagoranci da taimakom matasa a Gombe da ƙasa baki ɗaya.
A cewar Abdullahi, duk wani yunkuri na jawo hankalin ministan ya fito takarar gwamna ya gagara, inda ya ƙara da cewa sun yi amanna cewa Ministan ne ya fi da cewa ya karbi jihar.
Ya ce: “Domin tabbatar da abin da muke nufi dagaske ne yasa zami amfani da doka wajen tilasta wa Farfesa Isa Pantami ya fito takara a fafata da shi a zaɓen fidda gwani na kowace jam’iyga yake so.”
“Mutane 114 daga yankuna 114 da muke da su a Gombe, mun yanke siya masa Fam ɗin takara. Muna fatan wannan ƙara ta fargar da jagoran mu, Pantami.”
Kazalika ya bayyana cewa nasarorin da Pantami ya samu a tarihi yasa suka ɗauki wannan matakin domin jawo hankalinsa.