Amurka ta ce babu yaki tsakaninta da Iran
Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu cewa Amurka ba za ta shiga martanin da Isra’ilan ke son mayarwa kan Iran ba, acewar majiyar fadar White House.
Kasar Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan kasar Isra’ila a ranar Asabar, a wani martani na ramuwar gayya kan harin da Isra’ilan ta kai ofishin karamin jakadancinta da ke kasar Siriya.
Majiyar Amurkan ta kara da cewa Isra’ila tana da damar kare kanta daga duk wata barazana daga Siriya, kai harma da sauran kasashen duniya, wannan na daga cikin manufofin tsaron kasar, to amma Amurka ba za ta shiga cikin rikicin kai tsaye ba
Mai magana da yawun fadar White House kan tsaron kasa, John Kirby, ya shaidawa kafar yada labaran ABC cewa Amurka za ta ci gaba da tallafawa Isra’ila domin ta kare kan ta amma ba ta son shiga yaki da Iran.
DW Hausa