Labarai
Majalisar dattijan Najeriya ta amince da kudurin hana yanka jakuna a kasar
Advertisment
Majalisar dattijan Najeriya ta amince da kudurin hana yanka jakuna da kuma safararsu zuwa kasashen ketare.
Majalisar ta amince da kudurin ne bayan bayan tsallake karatu na biyu da ya yi.
Kudurin wanda shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Yahaya Abdullahi ne ya gabatar da kudurin wanda kuma ya samu amincewar majalisar a zamanta na ranar Talata.
Bbchausa na ruwaito cewa jinsin jakuna na fuskantar karewa ne a kasar saboda aikin wasu marasa kishin kasa da ke safarar jakunan zuwa kasashen ketare.
Akwai jinsin dabbobi da dama da a baya ake da su amma a yau suna fuskantar barazanar karewa.
Kuma masana ilimin gandun daji na cewa dabbobin da aka rayu da su shekaru 1,000 baya yanzu babu burbushin da yawa daga cikinsu.
https://bbc.in/3hCbibK