Kaf Afrika Babu Kasar Data Kai Najeriya Arhar Man Fetur ~ Lai Mohammed
Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya bayyana cewa farashin fetur a Nijeriya har a yanzu shine mafi karanta a kasashen yammaci da tsakiyar Afrika.
Rariya ta wallafa cewa Ministan ya bayyana hakan a yayin jawabi ga manema labarai na hadin guiwa wanda ministan wutar lantarki, Saleh Mamman da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva suka hada.
Lai Mohammed ya ce , duk da halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki, gwamnati ta ci gaba da aiwatar da manyan ayyukanta ballantana biyan albashi. Amma kuma dole ne ta cire wa kanta al’adun da za su durkusar mata da tattalin arzikinta.
Lai Mohammed ya kara da cewa, zamanin tallafin man fetur ya zo karshe a watan Maris na 2020 bayan sanarwar hukumar daidaita farashin kayayyaki. Gwamnati ba za ta iya bada tallafin man fetur ba saboda bata ganin daidai a hakan. Yawaita neman man fetur yanzu ya zama tarihi a Najeriya.