Labarai

Na hango za a kara shiga wahala a Nijeriya – Primate Ayodele

Shugaban cocin INRI Evangelical Church, Primate Ayodele ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ya canza salonsa na farfado da tabarbarewar tattalin arziki saboda har yanzu akwai tarin matsalolin a fannin tattalin arziki a Nijeriya.

Dclhausa na ruwaito cewa, Ayodele ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin ya sanya wa hannu

Ya bayyana cewa har yanzu abubuwa za su ci gaba da tsada kuma za a kara samun hauhawar farashin kayayyaki matukar gwamnati ba ta inganta harkar noma da tabbatar da samar da man fetur mai sauki da kuma ci gaba da samar da wuraren da za rika tace man fetur a kasar.

 

Wani labari : An lissafto Sanatocin Katsina da Kano da ba su gabatar da kudirin doka a zauren majalisa ta 10 ba

 

Daga cikin Sanatocin kamar yadda binciken jaridar Daily Trust ya nuna, akwai Sanata Rufa’i Hanga da ke wakiltar Kano ta tsakiya da Sanata Abdul’aziz Musa Yar’adua da ke wakiltar Katsina ta tsakiya da Sanata Muntari Dandutse da ke wakiltar Katsina ta Kudu.

Kazalika binciken ya gano tsoffin Gwamnoni 4 da ke zauren majalisar yanzu haka da ba su gabatar da kudirin doka ko daya ba tun da aka rantsar da majalisar, daga cikin akwai Abdul’aziz Yari daga jihar Zamfara, Adams Oshimhole daga jihar Edo da Simon Lalong daga jihar Plateau.

A majalisa ta 10 dai akwai tsoffin Gwamnoni 13 da suka yi nasarar zama sanatoci bayan sun kammala wa’adin mulkinsu na gwamnoni. Daga cikinsu akwai shugaban majalisar dattawan Godswill Akpabio daga Akwa Ibom da Abdul’aziz Yari daga jihar Zamfara da Aliyu Wamakko daga Sokoto da Aminu Tambuwal daga Sokoto.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button