LabaraiAddini

Nadin mataimakin Gumi: Masallacin Sultan Bello ba na sheikh Gumi ko iyalansa ba ne – Bida

Advertisment

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta ce Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna ba na zuriyar Sheikh Ahmed Gumi ba ne, na al’ummar Musulmi ne da ke karkashin kulawar kungiyar (JNI).

Kamfanin Dillancin labarai ta buga cewa Sakataren gudanarwa na JNI Yusuf Bida ya bayyana haka a ranar Litinin a Kaduna a lokacin da yake zantawa da manema labarai dangane da wani rubutu da aka yi a shafukan sada zumunta kan nadin mataimakin Sheikh Gumi.

Rubutun wanda wani almajiri kuma dalibin sheikh Gumi ya yi, ya jaddada cewa sabon mataimakin masallacin ba irin akidar sheikh Gumi ne ya ke da shi ba kuma bai bin mazhabonin sa.

A cewar Bida, an yi rubutun ne domin tunzura jama’a da haifar da hargitsi a masallacin da aka dade ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Bida ya bayyana cewa, nadin limamai da mataimaka a masallacin ya kasance ne bisa bukatar masu sha’awar da kuma jarabawar da JNI ta ke yi don tabbatar da cancantar wanda za a naɗa

Ya ce bayan an kammala jarrabawar sai a nada wanda ya fi kowa cancanta a matsayin limami ko mataimakinsa a masallaci.

Bida ya ce, “ Wannan hanya aka bi har aka samu fitowar Sheikh Ahmed Gumi wanda shi ne malamain da ke tafsiri a Masallacin.

A dalilin haka Bida ya yi kira ga daliban Gumi da su kwantar da hankulan su sannan su ci gaba da gudanar d al’nuran su cewa za a tabbatar da ba a samu rudaɗi akai ba.

Premium Times Hausa

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button