Ƴan bindiga sun sake sace mutum 61 a Kaduna


Ƴanbindiga sun sace kimanin mutum 61 a karamar hukumar Kajuru da ke jihar Kaduna, arewa maso yammacin Najeriya.
Ƴanbindigar sun kai harin ne a garin Buda ranar Litinin da daddare suka buɗa wuta, kamar yadda wasu mazauna yankin suka shaida wa BBC.
Sai dai babu wata sanarwa daga hukumomin jihar da jami’an ƴansanda da ke tabbatar da harin.
Amma mazauna yankin sun ce ƴanbindigar sun yi wa garin ƙawanya ne da misalin karfe 11:30 na dare suka dinga harbi kan mai uwa da wabi.
“Ba wanda zai iya fadin adadin ƴanbindigar da suka zo suka tattara maza da mata, waɗanda suka kai kusan mutum 61 da suka tafi da su,” kamar yadda wani mazauni garin ya shaida wa BBC.
Ya ce akwai ƴan’uwansa mutum shida cikin waɗanda ƴanbindigar suka tafi da su.
“Mun tantance mata 32 da maza 29 ke hannun ƴanbindigar kuma akwai mai jego cikin matan da suka tafi da su wadda ba ta wuce kwana huɗu da haihuwa inda suka tafi da ita suka bar jaririn,” in ji shi.
Ya ce ƴanbindigar sun abka garin ne da niyyar tattara mutane da dama amma taimakon jami’an tsaro da suka kawo ɗauki ne ya taƙaita yawan mutanen da suka sace.
“Ƴanbindigar na cikin tattara mutane sai ga jami’an tsaro sojoji na Kajuru suka buɗe wa ma su wuta suka dinga musayar wuta.”
“Ba don shigowar jami’an tsaro ba da ba a san yawan mutanen da za su ɗiba ba,” in ji shi.
Ya ce an samu tsaikun samun labarin al’amarin sakamakon rashin hanyar sadarwa ta layin salula a yankin.
BBC Hausa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






