Addini

Tsokaci akan amfani da carbi Wajen Tasbihi – Dr. Kabir Asgar

Advertisment

1. Malamai sun yi saɓani wajen fahimtar matsayin amfani da carbi a wajen ƙirgar tasbihi da sauran zikirori. Akwai malaman da suke da ra’ayin hanawa saboda Manzon Allah (SAW) bai yi amfani da carbi ba. Bugu da ƙari kuma ya yi umarni da a yi amfani da yatsu wajen ƙirgen. Kan gaba cikin masu wannan fahimtar akwai Sheikh Bakar Abu-Zaid da Sheikh Nasirudden Albaniy.

2. Ɓangare na biyu na malamai sune masu halasta amfani da carbi ga wanda ya ga yana da buƙata. A fahimtar waɗannan malaman, shi carbi kayan aiki ne kawai, ba shi da bambanci da sauran ababen da ake amfani da su wajen sauwake ayyuka. Wannan ita ce fatawar Allama Ibnu Bazz da Sheikh Uthaymeen. Kafin su kuma Shehkul Islam Ibnu Taimiyah ma tafi akan halasci ne, sai kuma Al-Imam as-Suyutiy wanda ya shahara da goyon bayan halascin.

Tsokaci akan amfani da carbi Wajen Tasbihi - Dr. Kabir Asgar
Tsokaci akan amfani da carbi Wajen Tasbihi – Dr. Kabir Asgar Asalin Hoto : Dr.kabir Asgar

3. Yadda manyan malaman nan na duniya suka sami saɓani akan mas’alar haka ma malamanmu nagida Nigeria suka saɓa wajen kallon mas’alar. A cikin malamanmu akwai masu halastawa da kuma masu bidi’antar da carbi.

4. Yana da kyau mu sani cewa an sami sahabbai da dama suna amfani da tsakwankwami ko ƙwallon dabino ko makamantansu wajen ƙirge a lokacin zikiri ko tasbihi. Daga cikinsu akwai Abud-Darda’ da Abu-Hurayra da Sa’ad. Sai dai su ba su kasance suna yawo da carbin ko su rataya shi a wuya ko makamancin haka ba. Suna barin carbin nasu ne a gida inda suke zama su yi zikirorinsu.

5. Wani abin lura shine, dukan ɓangarorin biyu na malamai sun dace da juna wajen cewa ƙirga tasbihi da yatsu shine ya yi, saboda shine ya dace da aikin Manzon Allah (SAW). Sai dai kuma samun wasu sahabbai na amfani da carbin ba tare da tsangwama ba, ya nuna sassaucin hakan ga mai buƙata.

6. A ƙa’idar ilimi, ba aibi bane don malami ya tafi izuwa ga wani ra’ayi akan wata mas’ala sannan kuma daga baya ya riski cewa akasin ra’ayinsa ne ya fi ƙwarin dalili, saboda haka ya canza matsayarsa. Hasalima, wannan abin yabawa ne da alamta adalcin malamin da tabbatar da cewa yana ci gaba da neman ilimi da bincike.

7. Har ila yau, mas’aloli ire-iren waɗannan waɗanda aka sami bambancin fahimta game da su, ba a mu’amalantarsu da ɗaukan zafi ko sukar wanda ya saɓa wa ra’ayinka ko tuhumarsa da son zuciya. Ba shakka al’ummarmu tana da buƙata izuwa ga riƙo da ladubban saɓani.

8. Ita harkar ilimi malamai ake bar ma ita. Ba daidai bane sauran mutane da ƙananan ɗalibai su dinga yin katsalandan cikin mas’alolin ilimi. Wannan tozarta ilimi ne da ɗaukar wa kai ɗaukakka. Ya kamata mu dinga yi wa kanmu adalci wajen auna nauyinmu da cancanta ko rashin cancantar tsoma bakunanmu akan mas’alolin ilimi.

Allah Ubangiji ya sa mu dace

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button