Mata su sha maganin ƙara girman mama “Nono” da mazaunai “Duwawu”don birge mazajensu hala ne – Sheikh Ibrahim Khalil


Halak ne Mata su nemi maganin kara girman Mama da Mazaunai don birge mazajensu ta hanyar amfani da maganin da Likitoci suka amince a cikin wata zantawa da yayi da gidan rediyon freedom radio kano inda ake yiwa malam tambayoyi yana bada amsa.
“Idan mace ta canza Hallita ta koma namiji ko namiji ya koma mace wannan haramun ne, Mace na son ta ƙarawa mamanta su zama manya ko su zama ƙanana ko su zama matsakaita ko su zama mai gidan tasa wannan ba dai-dai bane, saboda mijinta ko tana son ta samu miji ko duwawunta ya zama manya ko su zama ƙanana wannan duk bazai zamo laifi ba.
Wannan sun dogara da abinda likitoci sun ka gani wajen cutuwarsu, amma a canza namiji ya koma mace ko mace ta koma namiji kai tsaye wannan haramun ne, amma a canza hallita ta zama yadda namiji yake so misali kamar yadda Micheal Jackson yaso ya canza hallitarsa zuwa kanwarsa ko yadda ake a kasashen duniya yadda mace take so a karamata manyan duwawu ko a ƙara mata nonuwa a sanya soso, wannan shi laifi ne domin akwai yaudara namiji, amma idan ba soso bane nonon ne aka mayar haka ko duwawun anka mayar haka kaga wannan ba komai.
Wannan duk magunguna da ake sha basu da laifi sai dai ana bawa mutane shawara su je su nemi shawarar likitoci, in ba haka ba zasu je su sha abinda zai cutar da rayuwar su.- inji sheikh Khalil.