Gwamnatin tarayya za ta kara wa’adin shirin daukar mutane 77400 aiki a Nigeria
Daga Yahya Abdullahi Birnin Gwari.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana duba yiwuwar kara wa’adin ayyuka 774,000 da za ta dauka zuwa fiye da watanni uku
– Karamin ministan kwadago da dibar ma’aikata, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan
– Ya ce wannan sabon hukunci ya billo ne bayan korafe-korafen cewa aikin na wa’adin watanni ukun ba lallai ne ya kawo wani sauyi ga wadanda suka amfana ba
– Keyamo ya nuna karfin gwiwar cewa shirin daukar ayyuka na musamman (SPW) zai cimma nasara
Gwamnatin tarayya na duba yiwuwar tsawaita wa’adin diban ma’aikata 774,000 zuwa fiye da watanni uku.
Karamin ministan kwadago da diban ma’aikata, Festus Keyamo ya fada ma jaridar the Nation a ranar Litinin, 31 ga watan Agusta, cewa gwamnatin na iya mayar da aikin a matsayin shiri na shekara.
Ya ce wannan sabon hukunci ya billo ne bayan korafe-korafen cewa aikin na wa’adin watanni ukun ba lallai ne ya kawo wani sauyi ga wadanda suka amfana ba.
Ministan ya kuma nuna karfin gwiwar cewa shirin ayyukan na musamman, wanda zai samar da ayyukan yi ga mutum 774,000 zai cimma nasara.
Ina da tabbacin cewa shirin SPW zai cimma nasara dari bisa dari. Mun takaita shirin ne zuwa watanni uku ga ma’aikata 774,000 saboda shiri ne mai tsada kuma muna fuskantar faduwa a kudaden shiga,” in ji shi.
“Akwai dabaru da dama da gwamnati ke tattaunawa a kai. Baya ga haka, gwamnatin na iya tsawaita wa’adin shirin domin mayar dashi na tsawon shekara guda.”