Labarai

Har yanzu Nijar ba ta bude boda ba

Advertisment

Nijar ta hana a tsallaka iyakarta, sa’o’i 72 bayan sanar da bude boda kasar da Nijeriya kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito

Har ya zuwa yanzu dai hukumomin Jamhuriyar Nijar din ba su ce uffan ba game da wannan mataki na gwamnatin Nijeriya, kamar yadda majiyarmu ta jaridar dclhausa na ruwaito

Hukumomin Nijeriya irinsu na Kwastam da na kula da shige da fice na Immigration, sun sassauta hanyoyin shiga da fitar, amma na Jamhuriyar Nijar ba su yi hakan ba.

 

A ranar 13 ga watan Maris din nan dai ne fadar shugaban Nijeriya ta sanar da bude iyakokin kasa da na sararin samaniya ga Jamhuriyar Nijar tare da janye mata takunkuman da aka kakaba mata tun bayan da aka samu samu juyin mulki da ya yi sanadiyyar hambarar da gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohammed.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button