Labarai

Hotunan Gine-Gine 10 mafi Darajar kudi a fadin Duniya, Ka’aba ne na 1

MSN Money kungiya ce da ke kula da hada-hadar kudi, hannayen jari, kadarori da kuma lamuni a duniya.
Ta yi bincike a kan gini 30 mafi tsada da darajar kudi a fadin duniya kuma kasar Saudiya ce a kan gaba da gine-gine biyu. Ga dai jerin gini 10 mafi darajar kudi a duniya tare da hotunansu.
1. Masallacin Ka’aba, Makkah: Dala biliyan 100

Wannan shine wuri mafi tsari a Musulunci kuma mafi girma a Masallatan duniya.
Yana daukar jama’a sama da miliyan hudu a lokutan aikin Hajji. Darajarsa ta kai dala biliyan 100.
Masu kiyasi suna ganin akwai matukar wahala a samu ginin da zai wuce shi a daraja a fadin duniya koda kuwa nan gaba.
2. Ginin Abraj Al Bait, Makkah: Dala biliyan 16

Wannan ginin an kammala shi a 2012 kuma an yi shi ne domin mahajjata musamman shugabannin duniya da masu hannu da shuni. Baya ga tsananin tsadarsa, yana da fuskar agogo mafi girma a duniya.
Wannan ginin yana nan a garin Makkah da ke kasar Saudi Arabia.
3. Wurin shaƙatawa Marina Bay Sands, Singapore: Dala biliyan 6.2

Wurin shakatawa na Marina Bay Sands da ke Singapore ya kasance katafaren wuri mai dakunan alfarma.
An kammala gininsa a 2010 kuma tabbas a halin yanzu darajarsa ta karu.
4. Hedikwatar kamfanin Apple, Cupertino: Dala biliyan biyar

Wannan ginin yana birnin California da ke kasar Amurka kuma shine gini na hudu mafi tsada a duniya.
Kamfanin Apple yana da matukar tsada domin kuwa rarar kudinsa ta fi ta wasu kasashe masu tasowa a duniya.
Hakan ne yasa ba za a yi mamaki ba idan kamfanin ya kashe makuden kudade wurin gina hedkwatarsa.
 
5. Ginin Cosmopolitan, Las Vegas: Dala biliyan 4.4

Otal na Cosmopolitan yana da dakunan da yawansu ya kai 3,027 kuma ya lashe kudi har dala 3.9. Akwai babban wurin caca da dakin taro mai kujeru 3,200.
6. Sabon ginin cibiyar hada-hadar kasuwanci ta duniya, New York: Dala biliyan 4.1

Wannan ginin ya fi kowanne gini girma a kasar Amurka. yana da tsawon kafa 1,776 kuma shine na shida mafi tsada a duniya. An kammala ginin a 2012 a kan kudi dala biliyan 3.8
7.Ginin majalisar Bucharest: Dala biliyan 3.9

Gini ne wanda aka fara a 1984. A halin yanzu darajarsa ta kai jimillar kuɗi dala biliyan 3.9. Ginin yana nan ƙasar Romaniya.
 
8.Ginin Otel na Emirates Palace, Abu Dhabi: Dala biliyan 3.8

Otal na emirates yana kamanceceniya da fadar sarki a Dubai kuma yana da masauki 397 tare da katafarun wuraren shakatawa da na cin abinci.
An kammala ginin a 2005 kuma ya kai darajar dala biliyan 3, akwai yuwuwar darajarsa a yanzu ta haura hakan.
9. Wurin shaƙatawa na Wynn Resort, Las Vegas: Dala biliyan 3.4

Wannan wuri yana daya daga cikin manyan otal na duniya. yana da rukunin dakuna da wurin caca. An kaddamar da shi a 2005 a Wyn. Yana da dakuna 2,1716
10. Fadar Sarkin Brunei Istana Nurul Iman: Dala biliyan 3.3

An yi ginin a 1984 a kan kudi dala biliyan 1.4. Fadar ita ce masarauta mafi girma a duniya. Tana da yawan dakuna 1,788 da manyan dakunan taro 5,000.
Sources: Legithausa

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button