Labarai
An bude shagon barasa na farko a ƙasar Saudiyya
Advertisment


An bude shagon shan barasa a kasar Saudiyya, irinsa na farko a tsawon shekarau 70.
An dai takaice shagunan ne ga jami’an huldar jakadancin kasashe da ke Saudiyyar.
Ana dai yi wa wannan mataki kallon wani kokari a kasar da ta haramta sayar da shan barasa tun shekarar 1952.
BBC ta ruwaito cewa, Tun dai a watan Janairu ne kasar ta sanar da cewa za ta bude shagunan sayar da barasa ga wasu kayyadaddun mutanen da ba Musulmi ba a birnin Riyadh.
Yanzu dai jama’a na dasa ayar tambaya ga yunkurin kasar ta Saudiyya, inda suke neman sanin ko dai akwai yiwuwar kara fadada damar shan barasa a kasar fiye da takaice shi ga jami’an huldar jakadanci?
BBC Hausa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





