Labarai

Ƴan Bindiga sun sace ɗaliban makarantar tsangaya a jihar Sakkwato

Advertisment

Ana fargabar cewa ’yan bindiga sun sace ɗaliban wata Tsangaya a ƙauyen Gidan Bakuso da ke Karamar Hukumar Gada ta Jihar Sakkwato.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, maharan sun sace ɗaliban ne da misalin ƙarfe 1:10 na dare wayewar garin Asabar.

Shugaban makarantar, Liman Abubakar, ya ce kawo yanzu an nemi ɗalibai 15 an rasa, sai dai ya ce ba su tabbatar da adadin ɗaliban da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su ba.

Liman Abubakar ya kara da cewa, wannan ba shi ne karon farko da ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen ba amma ba a taba sace dalibansu ba sai yanzu.

Advertisment

Aminiya na ruwaito cewa ,dan majalisar mai wakiltar mazabar Gada- Gabas a majalisar dokokin jihar, Kabiru Dauda yayin da yake tabbatar da faruwar harin, ya ce ya samu kira daga ƙauyen da misalin ƙarfe biyu na dare cewa ’yan bindiga sun mamaye su.

“Na tuntubi mahukuntan kananan hukumomi da jami’an tsaro kuma na tabbata suna yin wani abu a kai.

Wakilinmu ya kuma samu labarin cewa, ’yan bindiga sun kai hari tare da kashe mutum uku a ƙauyen Turba da ke Karamar Hukumar Isa, ciki har da dagacin kauyen.

Wani mamba mai wakiltar mazabar Isa, Habibu Modachi wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce yana kyautata zaton harin na ramuwar gayya ne bayan da jami’an tsaro suka kai farmaki maboyar ‘yan bindigar kwanaki biyu da suka gabata.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Sakkwato, ASP Ahmad Rufa’i, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, amma zai tuntubi jami’in ‘yan sandan shiyya na kananan hukumomin biyu.

~Aminiya

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button