Abun takaici ne yadda wasu ke murna kan faduwar darajar Naira – Shettima
Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima, ya nuna rashin jin dadinsa game da martanin da wasu ‘yan Najeriya suka yi na murna kan faduwar darajar Naira.
A yayin da yake magana kan kalubalen tattalin arziki da kasar ke fuskanta, Shettima ya soki masu dariyar a matsayin ‘mararsa kishin ƙasa.’
Mahanga ta rahoto a cewarsa “A lokacinda Dala 1 ta koma fiye da Naira 1000 a madadin mu taru mu nuna alhininmu amma abun takaici sai wasu suka riƙa murna a shafin twitter suna jin dadin faruwar hakan. Wannan rashin kishin ƙasa ne” inji Shi.
Wani labari : Najeriya tayi sa’a ba a fara wasa da ni ba – inji Aboubakar
An ruwaito babban dan wasan Cameroon Vincent Aboubakar na cewa sai da ya roƙi mai horas da su akan ya sanya shi tun a farkon wasan Cameroon da Najeriya don yayi maganin Super Eagles amma hakan bai faru ba,
Vincent Aboubakar ya ce “Na roƙi kocina ya saka ni tun a farkon wasan mu da Najeriya a fara wasan dani duk da cewa na dawo daga jinyar rauni amma bai yi hakan ba.
Najeriya tayi sa’a da ba a fara wasa da ni ba…”
A wasan dai an tashi Super Eagles na Najeriya sun ci Cameroon 2 ba ko daya wato Nigeria 2 : 0 Cameroon
Duk da cewa an sako Vincent Aboubakar a zangon wasa na biyu wato bayan hutun rabin lokaci (Half-time) amma dai duk da haka shigarsa bata sauya komi ba