Tinubu ya naɗa shugabar sabuwar ma’aikatar taimakon al’umma


Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Delu Yakubu a matsayin shugaba ta farko a sabuwar ma’aikatar taimakon al’umma mai suna National Social Investment Programs Agency, NSIPA.
Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a yau Alhamis a Abuja, ta ce nadin ya dogara ne da amincewar majalisar dattawa.


An sanyawa dokar kafa Ma’aikatar Shirye-shiryen Taimakon Al’umma, NSIPA, (Establishment) Dokar, 2023, a ranar 22 ga Mayu.
Mrs Yakubu ta samu digirin digirgir a fannin aikin noma daga Jami’ar Jiha ta Fasahar Bio-Technology da ke Kharkiv, Ukraine, tare da gogewar sama da shekaru 15 a fannin Gudanar da Shirye-shiryen Taimakon Al’umma.
Shugaban ya umurci sabuwar shugabar da ta kasance jajirtacciya, nuna gaskiya, da samar da ayyuka masu inganci a NSIPA bisa kudurinsa na aiwatar da ajandar sabuwar rayuwa.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




