Labarai

Shugaba Buhari ya halarci taron bude Masallacin Izalah a Abuja, nan ya Sallaci Juma’a

Advertisment

Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron bude sabon Masallacin da kungiyar da’awa ta addinin Musulunci, Jama’atu Izalatul Bid’a Wa iqaamatus Sunna JIBWIS ta gina a birnin tarayya Abuja,jaridar legit na ruwaito.
An bude Masallacin ne yau Juma’a, 25 ga Maris, 2022
Shugaba Muhammadu Buhari ne babban bako na musamman a taron bude Masallacin.
Daga cikin wadanda suka halarci taron bude Masallacin akwai shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan; Kwamishanan ilimi na biyu na jihar Kano, Alaramma Ahmed Sulaiman, dss.
Kalli bidiyon.

Izalah ta gina katafaren Masallaci da kudin fatun layya a Abuja
Mun kawo muku rahoton cewa kungiyar JIBWIS za ta bude sabon Masallacin da ta gina a birnin tarayya Abuja ranar Juma’a.
Jibwis a jawabin da ta saki ranar Talata ta bayyana cewa an gina ne da kudaden fatun layya da mutane ke badawa fisabilillah.
Izalah ta bayyana hotunan Masalaccin dake unguwar Utako, kwaryar garin Abuja.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button