Labarai

An bindige Limami a bakin kofar masallaci a Amurika ya rasu

Advertisment

Wani limamin da aka harba jiya Laraba a ƙofar wani masallaci a birnin New Jersey ya rasu,

An bude wuta kan Hassan Sharif a kusa da wani masallaci dake Newark, a New York, inda aka gaggauta kai shi asibiti kafin daga baya ya mutu, in ji Atoni Janar na New Jersey Matt Platkin.

A cewar babban mai shigar da kara na Amurkan “Har yanzu basu san dalilin kai masa wannan mummunan hari ba amma shaidun da aka tattara zuwa yanzu ba su nuna cewa harin nada alaka da ta’addanci ba,” in ji Platkin.

Wakiliya ta ruwaito Akalla Amurkawa musulmi fiye da 300,000 ke rayuwa a jihar New Jersey wanda a yanzu suna cikin fargaba domin tun bayan barkewar yakin Isra’ila da Hamas, ake samun karuwar hare-haren kyamar Musulunci da kyamar Yahudawa a fadin Amurka.

Mai gabatar da kara na gundumar Essex, Ted Stephens, ya ce “Mun himmatu wajen tabbatar da adalci ga iyalan limamin,”

Margayin tsohon ma’aikaci ne a Hukumar Tsaron Sufuri ta Amurka (TSA) kuma hukumar ta tabbatar da cewa Sharif ya yi aiki a matsayin mai bada tsaro a filin jirgin saman Newark tun a shekarar 2016.

Lisa Farbstein, mai magana da yawun TSA ta ce “Mun yi matukar bakin ciki da samun labarin rasuwarsa tare da mika ta’aziyyarmu ga danginsa, abokansa da abokan aikinsa.”

A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar kula da yancin musulmi ta ƙasar, CAIR ta bayyana Sharif a matsayin “jagora nagartacce.”

Sannan kungiyar ta ja kunnen musulmi a yankin “Muna ba masallatai shawara da su bude kofofinsu amma su yi taka-tsan-tsan musamman ganin yadda a baya-bayan nan abubuwa ke kara tabarbarewa na kyamar musulmi,” inji kungiyar.

~wakiliya

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button