Labarai

Wani Malamin Firamare Ya Rataye Kansa A Jihar Kano

Advertisment

Rahotanni daga jihar Kano na cewa wani mutum mai suna Nuruddeen ya rataye kansa a unguwar Gadon Kaya da ke karamar hukumar Gwale a cikin birnin Kano.

Tun da farko ana zargin Nuruddeen da ke aikin sana’ar koyarwa a makarantar Prestige Academy ya yanke hukuncin rataye kan sa ne bayan da ya samu labarin tsohuwar matarsa ta sake aure.kamar yadda aminci Radio na ruwaito.

Wani Malamin Firamare Ya Rataye Kansa A Jihar Kano
Wani Malamin Firamare Ya Rataye Kansa A Jihar Kano

Tun da farko an tsinci gawar mamacin ne sakale a ɗaya daga cikin ajujuwan makarantaar ta Prestige da ke layin Damisa a unguwar ta Gadon Kaya.

Kawo lokacin haɗa wannan rahoton Tuni jami’an rundunarr yan sandan Kano ta dauki gawar mamacin domin faɗaɗa bincike.

 

Wani labari: DPO ya ƙi karɓar cin-hancin Naira miliyan 1 a hannun bandit din da ya kama

 

Wani DPO na ƴansanda ya ki amincewa da cin hancin naira miliyan daya da wani da ake zargin ɗan fashin jeji ne ya ba shi bayan an kama shi a wani otal da ke garin Kaduna.

Rahotanni sun bayyana cewa dan fashin jejin da aka kama ya bayar da cin hancin daga cikin kudin fansa da ƴansanda suka kwato daga hannunsa a wani otal da ke unguwar Tafa.

A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda a jihar, ASP Mansir Hassan, a yau Alhamis, an kama ɗan fashin jejin ne a ranar 19 ga watan Janairu, 2024.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button