Labarai

Akan ruwan rijiya makociya ta gutsere mata dan yatsa da cizo

Advertisment

Wannnan mata da kuke gani tana zaune a kaduna jihar kaduna da ke arewacin Nijeriya tana zaune a tudun wada ita da makwabciyar da suke haya,sai sunka je dibar ruwa sai rigima ta kaure wannan na cewa ita zata fara diba, Wannan na cewa ita zata fara diba sai fada ya kaure a tsakanin su sai daya ta samu Sa’a hannunta ya shiga bakinta ta gutsere mata dan yatsa, har abun dai ya kai su kotu sunan wadda abun ya faru da ita sunanta sha’awa na tu, AGG Multimedia services na samu wallafa wannan labarin a shafin su na
tiktok.

Inda ita wannan matar tayi bayanin zuwanta kotu.

Akan ruwan rijiya makociya ta gutsere mata dan yatsa da cizo

Na kawo makociya ta da abi min hakkina akan zalunta ta da tayi na cizo na na ciremin ɗan tsaya, daga diba ruwa ne saɓani ya shiga tsakanin mu har hannuna yakai bakin ta nayi nayi ta cire sai da ta cire yatsa akwai mutane a wurin bayan faruwa hakan na kira yan uwa suka zo sunka gani sai anka kira yan gidan gayu aka tafi da mu da ita.

Yanzu babu dan raguwar ɗan tsayar kenan

Babu shi domin ta riga ta cire da hakkorinta- inji sha’awanatu.

Daman bani na kawo karar kotu ba daga can gidan gayu ne anka ce ayi sulhu mijinta yace ba wani sulhu da za’ayi tunda fadan mutum biyu ne ba abunda zai biya akan asibiti da sauran su, yan uwa da makota suke taimawa ina zuwa asibiti ana duba ni domin mijina ba wani karfi yake da shi ba, saboda kullum ana wanke wa ɗari biyar ake biya kuɗin kula da hannun.

Bayan munje kotu alkali yace baza’a yi Shari’a ba sai a kai ta gadurum washe gari za’ayi, bayan anyi alkali yace sai sun aje dubu ɗari biyar ₦500,000, saboda kafin muzo shi mijin har ya dau lauya , shine alkali yace baza’a bayarda belinta ba sai sun aje dubu dari biyar da mai unguwa guda daya, da limamai gudu biyu, sai ni aka ce in tafi.

Bayan na tafi sai gashi bada jimawa ba shi mijin ya dawo da ita suna da shewa suna habaici suna cewa :

Ai su sunbi ta sama ne sun dawo ba abinda za’a yi musu, dan shi yasan mutane a sama , ni kuma bani da kowa.”

Wai yanzu bayan munje kotu, sunje high court sun shigar da kara, a dauki karar shine ankace in tafi wai 29 ga watan biyu an ƙara kwana wata.

ina rokon Allah ya shigemin lamarina , abimin hakkina.

Dan Allah ko bayan raina ina so a daukamin mataki domin zuciya ta na bugawa, ba lallai bane in kai wannan lokacin ba wallahi”

Ga bidiyon nan.

@agg_multimedia_servicesAkan ruwan rijiya makociya ta cirewa makociyar ta yatsa da cizo

♬ original sound – AGG Multimedia Services

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button