Tinubu ya dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar ma’aikatar NSIPA
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da dakatar da Halima Shehu a matsayin shugabar hukumar kula da shirin tallafawa marasa ƙarfi ta ƙasa, NSIPA.
Tashar talabijin ta Channels ce sanar da hakan a daya daga cikin shirye-shiryenta da safiyar yauTalata.
A cewar Channels, Tinubu ya bada umarnin dakatar war ta nan take.


Yayin da har yanzu ba a bayyana dalilin da ya sa aka dakatar da Halima Shehu ba, hakan na nuni da sauye-sauye a NSIPA, majiyarmu ta daily Nigerian ta jiyo mana wannan labari.
Hankali ya kai kan hukumar da ke da alhakin gudanar da muhimman shiri kamar su N-Power da shirin tura kuɗaɗe ga marasa galihu, sakamakon matsaloli da ke fitowa daga cikin ta.
A kwanakin baya ne dai masu cin gajiyar shirin N-Power suka gudanar da zanga-zangar lumana a wasu jihohin kasar saboda gaza biyan su alawus-alawus da gwamnatin tarayya ta yi.
Tinubu ne ya nada Shehu a watan Oktoba 2023, kuma Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin nata a ranar 18 ga Oktoba, 2023.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





