Labarai

Babban bakin Najeriya zai mayar da wasu sassan zuwa jihar legas

Advertisment

Babban bankin Najeriya na shirin mayar da wasu sassan sa zuwa babban birnin kasar na farko kuma cibiyar tattalin arzikin kasar, jihar Legas

An bayyana hakan a cikin wata sanarwa ta cikin gida da ake samu a ranar Lahadi

Jaridar PUNCH ta ranar Asabar ce ta fitar da labarin.

Matakin a cewar wani jami’in babban bankin wanda bai so a bayyana sunansa ba, shine na rage cunkoso a babban ofishin bankin da ke babban birnin tarayya.Babban bakin Najeriya zai mayar da wasu sassan zuwa jihar legas

Duk da cewa wasu ma’aikatan bankin sun nuna rashin amincewarsu da batun canza shekar tare da bayyana cewa ra’ayin kabilanci ne ya jawo hakan, amma majiyar ta yi ikirarin cewa an yi hakan ne domin
‘amincin ma’aikata da haɓaka yawan aiki.

Wani labari daban : Kwaɗayi ko Rashin imani : An kama barayin janareton masallaci a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun yi nasarar kama wasu mutane biyu da ake zarginsu da satar janareta da batirin da ke haska futilun masallaci mai amfani da hasken rana a wani masallaci da ke Kaduna.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar Mansir Hassan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Kaduna ranar Asabar.

Dclhausa na ruwaito cewa Mansir ya ce jami’an tsaro sun kama fara kama daya daga cikinsu mai suna Basiru Rabiu da ake zargin a unguwar Sabon Gari da ke karamar hukumar Hunkuyi.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button