Labarai
Wata mata ta shake diyarta yar shekara 7 har Lahira a cikin gonar rake (Hotuna)
Advertisment
Yan sanda a Uganda sun kama wata mata mai suna Tilutya Suzan da laifin kashe ‘yarta ‘yar shekara 7 mai suna Namugaya Mercy. Shafin Isiyaku na ruwaito
A cewar kafofin yada labaran kasar, mahaifiyar mai shekaru 35 ta shake diyarta har lahira tare da jefar da gawarta a gonar.
Rundunar ‘yan sandan Kakira ta cafke Tilutya domin ci gaba da bincike.