Labarai

Dan adaidaita sahu ya samu kyautar dubu dari 100 baya ya maida naira miliyan 9 da ya tsinta

Wani direban babur mai ƙafa uku, Ali Bulama daga kauyen Jumbam a karamar hukumar Tarmuwa ta jihar Yobe ya samu ladan Naira dubu 100 saboda hangen nesa da tsoron Allah da ya nuna wajen mayar da Naira miliyan N9 da ya tsinta ga mai shi.

Jaridar daily Nigerian hausa na ruwaito,Aji Jumbam, mai shekaru 35, ya ce mai kudin, mazaunin Maiduguri ya hau babur din sa ne a Jumbam da misalin karfe 9:30 na dare ranar 17 ga watan Nuwamba.

“Da misalin karfe 11:30 ne bayan na sauke shi na koma gida sai na ga buhu dauke da wasu kayayyaki da suka rage a babur nawa.

Dan adaidaita sahu ya samu kyautar dubu dari 100 baya ya maida naira miliyan 9 da ya tsinta
Dan adaidaita sahu ya samu kyautar dubu dari 100 baya ya maida naira miliyan 9 da ya tsinta

“Lokacin da na gano cewa buhun yana dauke da wasu kudi, sai na yi sauri na fita neman mai shi. Ya zuwa lokacin, tuni labarin bacewar Naira miliyan 9 ya bazu a kauyen.

“Bayan wani lokaci da taimakon wasu mutanen yankin, an gano mai kudin, Ni kuma na mika masa kudin,” inji shi.

Bulama, wanda ya dauki hayar keken mai uku, ya ce mai kudin ya ba shi Naira 20,000 tukwici.

Bulama ya kuma samu kyautar takardar shaidar girmamawa da kudi Naira dubu 100 ga Bulama, wanda Shugaban kungiyar sakatarorin dindindin na Yobe, Alhaji Maisandari Lawan mai ritaya ya ba shi, inda ya yaba wa matashin bisa gaskiya da tsoron Allah.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button