Labarai

Endsars : Shugaba Buhari Ya Yiwa Duniya Jawabin Abinda Yake Faruwa

Fassarar jawabin Buhari akan Endsars ga yan Nijeriya da duniya

Ga fassaran jawaban da Maigirma shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a takaice game da halin da Kasarmu Nigeria ta tsinci kanta a yau:
1- Anyi ta’adi da barna sosai a zanga-zangar ENDSARS, an lalata kayan gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu har da gidan babban basaraken jihar Lagos
2- Nayi takaicin rasa rayuka da aka samu a dalilin wannan zanga-zanga
3- An canza akalar zanga-zangar ta lumana zuwa wani abu dabam, wannan ba zamu lamunta ba dole za’ kare rayukan al’ummah da dukiyarsu
4- Ba zamu taba yadda da cewa zanga-zangar ta luma ce ake yi ba, domin duniya ta ga irin barnan da akayi
5- Labaran karya da ake ta yadawa a kafofin sada zumunta da kokarin kawar da gaskiya abin takaici ne
6- Duniya ta shaida game da kokarin da mukeyi wajen tabbatar da gaskiya da adalci, a dena dogaro da labaran karya wanda yake fitowa daga gurin ‘yan adawa ko masu muguwar manufa ga Nigeria
7- Wannan Gwamnati na kokarin kawo saukin rayuwa a cikin alummah
8- Muna da babban tsari na fitar da miliyoyin ‘yan Nigeria daga kangin talauci da duniya ta fuskanta a dalilin annobar Coronavirus
9- Mun ware kudi sama da naira bilyan 75 domin samar da aiki da sauki wa ‘yan kasa ba tare da bata lokaci ba, wannan na daga cikin kokarin da muke wajen samar da saukin rayuwa a Nigeria
10- Babu wata gwamnatin Demokaradiyyah a Nigeria da take kokarin kawo sauyi da adalci kamar wannan gwamnatin
11- Muna shirin tabbatar da sabon tsarin albashin ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro wanda zai biya bukatunsu bakin gwargwado
12- Mun kawo sabon tsarin albashi wa Malaman makaranta
13- Zamu cigaba da kawo tsari mai kyau a wannan gwamnatin
14- Zamu tabbatar da cewa an kare ‘yan Nigeria da dukiyoyinsu a wannan yanayi da ake ciki
15- A tuna gwamnati na da hakkin kare ‘yan kasa da dukiyarsu da daga kowani irin kalubale na ayyukan ta’addanci da tsageranci
16- Zuwa gareku kasashen waje da kuka nuna damuwa a kan mu, muna godiya, amma ku dinga lura da labarun karya da ake yadawa game da halin zanga-zangar ENDSARS
17- Ina rokon masu zanga-zanga da su lura da kokarin da muke wajen kawo sauyi a cikin kasa
18- Kada ku biye wa miyagu su kawo cikas da barazanan tsaro da taka dokokin kasa, ba zamu taba barin haka
19- Muna kira da a dakatar da zangar munji bukatunku, zamu biya
20- Ku bar zanga-zanga fita harkokinku na yau da kullun
21- Hukumomin tsaro zasu tabbatar da tsaronki da dukiyarku ba tare da zalunci ba
22- Muna ta’ziyya wa rundinar ‘yan sanda da iyalansu wadanda aka kashe a dalilin wannan zanga-zangar
23- Muna godiya ga gwamnonin Nigeria da shugabannin addini da na gargajiya
24- Wannan gwamnatin na kokarin girmama kowa, amma ba zata taba barin wadanda zasu kawo matsala a kasa su ci nasara ba
25- Allah Ka albarkaci kasarmu Nigeria
Majiyarmu ta samu daga shafin datti assalafy.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button