Labarai
Sojojin Najeriya sun ceto shetu bamai sangayama da boko haram na sace tun shekarar 2014
Advertisment
Dangin Shetu Bamai Sangayama (wacce ke jikin hoton da ake kasa) sun gano ta bayan da Dakarun Sojojin Najeriya suka ceto ta daga maɓoyar yan boko Haram a Bama dake jihar Borno.
Yan ta’addan sun sace ta tun watan Satumba a shekarar 2014 tare da ya’yan ta 4, mata 3 da namiji ɗaya.
Hoto na farko an dauke shi ne jiya yayin da dakarun sojin Najeriya suka ceto ta daga hannun yan ta’adda a Bama.
Advertisment


Hoto na 2 an dauke shi ne kafin Shekara ta 2014 da aka sace ta,


ragowar hotuna biyu na karshe kuma ƴaƴanta ne.




Rahoto: Aliyu Samba.