Labarai

‘Yan kato da gora sun kama mutanen da ke yin tsire da naman Kare

Jami’an ‘yan kato da gora ta kungiyar ‘yan bijilente a jihar Bauchi sun kama wasu mutane biyu a jihar wadanda suke yin tsire na sayarwa da naman Kare.

Wannan lamari dai ya faru ne a unguwar Yelwan Kagadama da ke jihar.

Mutanen wadanda sun dade suna wannan sana’a suna yaudarar mutane da cewa tsiren na naman Akuya ne.‘Yan kato da gora sun kama mutanen da ke yin tsire da naman Kare

Wakilin Gaskiya Ta Fi Kwabo ya jiyo cewa, za a mika mutanen biyu ga ‘Yan sanda domin ci gaba bincike.

Wani labari : Ƴan sanda sun saki miji, sunyi cafke wanda ake zargi da kashe matar aure a borno

Rundunar ƴansanda a jihar Borno, a jiya Talata ta ce ta saki mijin matar da aka kashe a gidan aurenta da ke Maiduguri bayan ta kama babban wanda ake zargi.

Rundunar ƴansandan ta ce an sako mijin marigayiyar, mai suna Adamu Ibrahim da abokinsa, Bukar Wadiya da aka tsare su bayan sun kai rahoton afkuwar kisan ga ƴansanda.

Daily Nigerian Hausa na ruwaito,Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta ASP Sani Kamilu.

Ya ce an bi sawun babban wanda ake zargin, Abacha Bukar tare da kama shi da laifin kisan matar mai suna Fatima Alhaji-Bukar mai shekaru 24 a ranar 18 ga watan Oktoba.

Kamilu ya ce ƴansanda sun kama wanda ake zargin ne bayan da suka bibiyi wayar marigayiyar da ya sace

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA