Kannywood

Bidiyon da ya sanya anka dakatar da Khadija mai numfashi daga kannywood

Advertisment

Wannan shine dalilin da yasa anka dakatar da jarumar Masana’atar Kannywood khadija mai munfashi wanda shine dai wanann bidiyo ayi shine a gidan rawa wanda anka fi sani da gidan gala.

Gidan gala gida ne wanda jaruman kannywood da mawaka suna zuwa da dama kadan daga cikin su ne basa zuwa wannan wajen domin duk harka ce ta neman kuɗi.

To wannan bidiyo na Khadija mai numfashi yayi matuƙar daukar hankalin mutane har wasu a manhajar titkok suke kira da hisbah su kama wannan yarinyar irin wannan abu da ta aikata domin wadda abun yayi yawa sosai.

Duba da irin korafe korafe da anka shigar a hukumar tace fina finai ta amsa kiran mutane inda sunka nemata da tazo domin kare kanta da kuma tsawatar mata akan irin wannan rawar ta banza amma kayi kunnen uwar shegu.

Ga bidiyon nan kasa..

An dakatar da Khadija amai numfashi daga harka fim – Abba elmustapha

Assalamu alaikum wato bidiyo ne ya yadu/bazu yadda suke zuwa suna raye raye na rashin kamun kai , na tozarci wanda babu daɗi kuma kowa yasan irin yadda korafe korafen da muke karba a koda yaushe mun kirata domin ta kare kanta, ya akayi tabari tana yar masana’atar kannywood da ake bata tarbiyya kada ta yarda tana irin wadannan abubuwan da zasu iya jawo cece kuce.

Wanda zai iya zamo illa ga al’ummar jihar kano, ko kuma makalla tanmu na shirye shiryen mu kada mu saka kanmu irin wadannan raye raye amma ta saki wannan bidiyo na gidan rawa, mun kirata domin muji daga gareta abun ya faskara.

Babban laifin da zakayiwa hukumar mu ,mu kiraka ka kasa gayyatarmu- inji abba almustapha.

Mun kirawo ta tace bata gari yaushe zaki dawo garin , ta dawo garin mun san tana garin tazo koda mu samu sasauci ne muji daga gareta koda mu tsawatar mata taki ta bari.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button