Failed State 2030 : Hasashen rushewar nigeria tun a 2011
A ƙarshen shekarar 2020 na karanta wani report wanda US Air Force suka fitar inda suka hasasho rushewar ƙasarmu Nigeria kafin ko zuwa shekarar 2030.
Sun yi wannan analysis ɗin ne a shekarar 2011 saboda su san matakin da US za ta ɗauka saboda rushewar Nigeria zai shafi tattalin arziƙin duniya.
Na kaɗu matuƙa a lokacin, saboda ina sa rai cewa ƙasarmu za ta gyaru tun da ƙuruciyarmu, ashe lamarin zai ƙara ta’azzara ne. A cikin report ɗin sun yi hasashen yawancin abubuwan da yake faruwa a Nigeria a halin yanzu, dalilin ƙiranta da “failed state” kenan tare da nuna cewa kafin shekarar 2030 za ta rushe.
Abubuwan da suka tattauna a cikin report ɗin zai ba ka tsoro. Bari in yi muku summary kamar haka:
—Za a shiga matsi na yunwa (abinci zai fi ƙarfin talaka) sanadiyyar sace dukiyar ƙasa da karyewar tattalin arziƙi
—Za a fuskanci mummunan rashin tsaro wanda zai addabi mutanen ƙasar musamman yankin Arewa
—Za a zo matakin da jami’an tsaro ba za su iya kwantar da tarzoma ba
—Gwamnati ba za ta iya biya wa mutanen ƙasar buƙatunsu ba
—Kidnapping zai zama ruwan dare. Bayan BH, za a samu wasu militant groups waɗanda za su addab mutane kuma su rikita ƙasar
—Faɗan addini da ƙabilanci zai ɓarke wanda zai iya kai wa ga faɗan basasa
—Sakamakon rashin aikin-yi, matasa za su zama ƴan zaman-kashe-wando kuma hakan zai haifar da criminal activities kamar sace-sace, kashe-kashe, da tashe-tashen hankula
—Saboda yawaitar population, zai zama cewa zai yi wuya iyaye su iya ɗaukar nauyin ƴaƴansu, kuma gwamnatoci za su zama ba su da ikon faɗa-a-ji
—Za a rinƙa amfani da addini da ƙabilanci a rinƙa yaudarar mutane a ɓangaren siyasa da tada tarzoma
—Yawancin matasan ƙasar za su koma rayuwa a yanar gizo da dandulan sada zumunta. Social media za ta ruɗe su sosai.
—Idan ƙasar ta rushe, US da wasu ƙasashen duniya za su shigo don samar da tsaro, wanzar da zaman lafiya, da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arziƙi
—Suka ba da shawara ga Shugaban US wanda zai zo a lokacin da hakan zai faru cewa idan US ta yanke shawarar shiga cikin wannan lamarin, to lallai ta yi gaggawar amfani da fasahohin zamani
—Idan US ta yarda za ta shiga cikin lamarin, suka ce to ta tabbatar ta samar da kayan aiki masu kyau na zamani tare da amfani da ƙarfin soji
—Bugu da ƙari, suka ce a Nigeria akwai haziƙan matasa da masu basira waɗanda idan suka samu goyon baya za su ba da mamaki
….bari in dakata a nan, sauran kuma sai kun karanta za ku gani.
WAƊANNE MATAKAI YA KAMATA GWAMNATIN NIGERIA TA ƊAUKA IDAN BA TA SO ƘASAR TA RUSHE?
Wannan ma analysis ɗinsu ne. Suka ce ga wasu matakan da gwamnatocin Nigeria ya kamata su ɗauka don hana faruwar haka:
1. Nigeria ta rage dogaro da man fetir. Misali, kuna ganin yadda suke ƙoƙarin sa wa Dangote hawan jini saboda oil business. Sannan yanzu talaka ya gane idan aka janye tallafin man fetir shi ake gasa wa aya a hannu
2. Nigeria ta rage corruption
3. A samar da ingantaccen tsaro
4. A inganta harkar ilimi sosai tare da samar wa matasa ayyuka
5. A inganta harkar fasaha, noma da ƙere-ƙere
Wannan kaɗan daga cikin abubuwan da na tsakuro muku ne. Ƴan’uwana bookworms za ku iya karanta cikakken report ɗin. Ga title ɗin za ku same shi a ResearchGate, “Failed State 2030: Nigeria – A Case Study”
Duk waɗannan abubuwan da na lissafo a sama ba molanka ba ne. A cikin report ɗin na karanta. A 2011 suka fitar da shi. Kai ma ka je ka karanta tunda ga sunansa a sama na ajiye kafin ka fara cewa ba haka ba ne.
A WANNE MATAKI MUKE YANZU?
A yanzu haka kaf cikin abubuwan da suka hasasho wanda na rubuto a sama babu wanda bai faru ba. Wannan zanga-zangar da ta ɓarke (Allah Ya taƙaita al’amura), da nuna halin ko-in-kula da mahukuntan ƙasa suka yi, ya nuna wata mummunar ɓarna da za ta faru kafin 2027.
—It is “unusual” a ga teenagers suna tare jami’an tsaro tare da jifansu. Wannan rashin tsoro na yara ƙanana “babban abun tsoro ne”. Rashin tsoro ne ya ba wa 1979 Iranian Revolution nasara. Ana harbinsu da bindiga, su ku ma suna mayar da martani da duwatsu.
—It is “uncultured” a ga jami’in tsaro (Police) yana harbin teenagers da under 25. Kenan an zo matakin da jami’an tsaro masu bindiga ba za su iya kwantar da tarzoma ba. Yau Chief of Army Staff ya ce suna dab da shiga lamarin. Kenan abun yana so ya fi ƙarfin Police duk da asarar rayuwa da ake yi kullum sakamakon harbin da suke yi.
—Waɗannan yaran da aka kashe iyayensu sakamakon rashin tsaro, da waɗanda aka banzatar a titi, da waɗanda aka kasa ba su ilimi da tarbiyya, da waɗanda aka hana su ayyukan-yi — tare da gasa musu aya a hannu ta hanyar talauci da yunwa, ba a fara ganin “mummunan outcomes” ɗinsu ba.
—Masu roƙon manyan ƙasa cewa su taimake su su gyara al’amura a Nigeria don talaka ya samu ya yi numfashi, ku yi sani cewa ba za su iya ba ko da sun so hakan.
—Malamai masu yi wa manyan ƙasa nasiha, ku yi sani cewa ba za su taɓa ɗauka ba ko da sun so hakan.
—Abun da ya kamata shugaba mai hangen nesa ya yi shi ne hango lokacin da za a kai talaka maƙura ko don tsira da kujerarsa. Saboda duk ranar da talaka ya yi bore babu wanda ya isa ya dakatar da shi ko da “bullet” ne.
—Daga yanzu har zuwa lokacin da ba a sani ba, zanga-zanga za ta ci gaba da ɓarkewa “uncontrollably” kuma babu wanda ya isa ya dakatar da hakan.
—A halin da ake ciki yanzu a Nigeria an take kan bodari ne, sannu a hankali tusar da yake sakewa mai tsananin ɗoyi sai ta buwayi kowa a ɗakin da aka kulle.
—Masu mulki da attajirai su guji fushin waɗannan matasan da aka banzatar da kuma talakan da ake gasa masa aya a hannu, “outcome” ɗin nan ba kyau zai yi ba.
—Yanzu talaka yana ganin shi ya zaɓo wannan wahalar shekarar da ta gabata, bai san cewa 2027 ma abun da zai ƙara faruwa ba kenan.
ME YA KAMATA MATASAN NIGERIA SU YI A HALIN YANZU DA ƘASA TAKE NEMAN RIKICEWA?
…..next
Marigayi Maitama Sule ya ce, “Behind every crisis anywhere in the world is injustice and the solution to that crisis is justice.”
— Muhammad Auwal Ahmad
CEO, Flowdiary
Ga link nan ga wanda ke son karanta research ɗin baki ɗaya: